Mutum 18 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Bauchi

IMG 20191212 WA0005
IMG 20191212 WA0005
Akalla mutum 18 ne suka kone kurmus a wani hasarin mota da ya rutsa da wata mota kirar Hiace bas da tirela a kauyen Nabardo a kan hanyar Bauchi zuwa Jos.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewar hatsarin ya faru ne da misalin karfe 4:40 na yamma a ranar Laraba.
“Abun takaici shi ne direban da duk fasinjojin motar sun kone kurmus.
“Hatsarin ya faru a cikin daji wajen da babu kowa ballantana a kawo wa wadanda abun ya rutsa da su dauki.
“Hatsarin yana aukuwa wuta ta tashi nan take, motar da duk wadanda ke cikinta suka kone kuma babu wanda za a iya ganewa,” in ji shi.
Abdullahi ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta yi musu jana’iza ta bai daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here