Hukumar da ke sa ido kan harkokin rarraba man fetur ta Najeriya ta rufe gidajen mai guda 14 bisa sai da mai sama da farashin da gwamnati ta amince.
Ko’odinetan hukumar a jihar Aliyu Muhammad-Sama ne ya bayyana hakan yayin rangadin zagaye da kuma sanya ido dasuka gudanar yau Alhamis a Kano.
Ya ce hukumar ta rufe gidajen man fetur bisa saida fetur akan Naira 295 da kuma Naira 300 kan kowace lita sama da farashin da aka amince da shi.
“Muna da tsauraran ka’idoji don hukunta masu laifin da suka hada da soke lasisin gudanar da aiki, sanya takunkumi, biyan hukuncin tara.
“A yanzu; za a sanya wa gidajen man da aka rufe su biya Naira 150,000 ga kowane injin bada mai fetur muddin suna son komawa kan farashin da ya dace da jama’a,” inji shi.
“Rashin adalci ne ace hukumar na biyan N45 a kowace lita na man fetur da suke jigila daga Legas ko fatakwal” in ji shi.
Sai dai ya ce manyan ‘yan kasuwa suna rarraba mai a kan Naira 185 kan kowace lita, ya kara da cewa hukumar ta rufe gidajen mai sama da 120 a jihar a watan Disambar 2022.













































