Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar kwara ya rantsar da Mai Shari’a Abiodun Ayodele Adebara a matsayin Mukaddashin Alkalin Alkalan Jihar Kwara, sa’o’i kadan bayan Mai Shari’a Suleiman Durosinlorun Kawu ya sauka daga kujerar.
Da yake jawabi yayin bikin rantsar da mukaddashin alkalin alkalan a Ilorin, gwamnan ya ce cigaban da aka samu ya kara tabbatar da mutunta gwamnatinsa na raba madafun iko da bin doka da oda.
“Na yi farin cikin samun karramawar da aka yi da yammacin yau na rantsar da Hon. Mai shari’a Abiodun Ayodele Adebara a matsayin mukaddashin babban alkalin jihar Kwara. Hakan ya biyo bayan ritayar da Hon. Justice S.D. Kawu, wanda shi ne babban alkalin jihar Kwara har zuwa jiya Laraba.
“Abin farin ciki ne a gare mu a jihar Kwara cewa akwai dangantaka mai jituwa tsakanin bangarorin gwamnati uku. Zaman lafiya da wannan ya haifar yana kara tabbatar da cewa lallai jihar Kwara Jiha ce ta Zaman Lafiya,” inji Gwamnan.
Babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a Barista Ibrahim Sulyman, a nasa bangaren, ya ce: “Mun taru a yau ne domin shaida aikin da kundin tsarin mulki ya ba Gwamnan Jihar Kwara kamar yadda sashe na 271 karamin sashe na 4 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.













































