Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe makarantu na Firamare, Sakandare da manyan makarantu a faɗin jihar saboda ƙarin matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankunan arewacin ƙasar.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Bauchi, Jalaludeen Usman, ya fitar ga manema labarai a Bauchi.
Sanarwar ta bayyana cewa rufe makarantun ya shafi makarantun gwamnati, na ƙananan hukumomi, na masu zaman kansu, da na gwamnatin tarayya, tare da fara aiki nan take.
Ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki wannan mataki ne bayan dogon shawarwari da kuma sakamakon ƙarin matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai da sauran al’ummomin makarantu a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnati ta fahimci cewar wannan mataki zai kawo cikas ga wasu, amma kare rayuwar yara shi ne babban alhakin da ya rataya a wuyan gwamnati.
Ya ƙara da cewa kowanne ɗalibi a jihar Bauchi ya cancanci ya yi karatu cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba.
Karanta: Garkuwa da Mutane: Gwamnatin jihar Neja ta umarci a rufe Makarantu sai abinda hali ya yi
Sanarwar ta roƙi iyaye, masu kula da ɗalibai, shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalinsu, su kuma kasance masu haɗin kai.
Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro domin magance matsalolin cikin gaggawa, sannan a dawo da ayyukan makarantu idan an tabbatar da tsaro.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa gwamnatin tarayya ta rufe wasu makarantu saboda ƙaruwa matsalar tsaro da sace ɗalibai.
Haka kuma jihohin Kwara, Filato, Neja, Benue da Katsina sun rufe makarantun su saboda irin wannan barazana.













































