Garkuwa da Mutane: Gwamnatin jihar Neja ta umarci a rufe Makarantu sai abinda hali ya yi

Bago 750x430

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantu a jihar nan take bayan sace yara daga makarantar Katolika dake Papiri, karamar hukumar Agwara.

Bago ya bayyana wannan mataki a yayin taron manema labarai bayan wani babban taron tsaro da aka gudanar a Minna ranar Asabar.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici wanda za a iya kaucewa sake faruwar sa.

Ya ce wannan ba lokaci bane na zargin juna, amma aikin yanzu shine mai da hankali kan ceto yaran da aka sace da sauran wadanda abin ya shafa.

Gwamnan ya yi kira ga hukumomin tsaro, kungiyoyin farar hula, kwadago da malaman addini da su hada kai wajen ganin an ceto duk wanda aka sace.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na da niyyar kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ya kara da cewa Najeriya ita ce kawai kasar da muke da ita, kuma Jihar Neja har yanzu ita jiharmu.

Karanta: Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci a gaggauta ceto ɗalibai Mata 328 da aka yi garkuwa da su a jihohin Niger da Kebbi

Bago ya bayyana cewa rufewar makarantu zai shafi na Firamare, Sakandare, masu zaman kansu, na addini, Kwalejin Gwamnatin Tarayya Minna, da makarantun koyon aikin jinya dake Bida da Kontagora.

Gwamnan ya ce rufewar zai ci gaba har sai an samu sabon umarni, kuma zai kasance kamar hutun Kirsimeti tun kafin lokaci saboda dalilan tsaro.

Har yanzu ba a tabbatar da adadin yaran da aka sace ba, yayin da hukumomin tsaro ke gudanar da bincike kafin a fitar da sanarwar hukuma daga baya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya tuna cewa, wasu da ake zargin yana bindiga ne sun sace wasu dalibai daga St Mary dake Papiri, karamar hukumar Agwara, a ranar Alhamis.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here