Hadarin mota ya yi sanadiyar ajalin mutane 19 tare da raunata 26 a Kano

C6658472 6A29 4CFE A680 817232AF4567
C6658472 6A29 4CFE A680 817232AF4567

Kimanin mutane 19 ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis a wani hatsarin mota da ya afku a Bagauda, kusa da harabar makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke kan titin Kano zuwa Zaria.

Solacebase ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne lokacin da wasu motocin bas na kasuwanci guda biyu – Toyota Hiace – masu lambar rijista KBT 152 XA da NSR 275 ZX suka yi karo.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar Kano, Zubairu Mato, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce hatsarin da ya rutsa da fasinjoji arba’in da biyar ya yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha tara yayin da wasu ashirin da shida suka samu raunuka daban-daban.

Mato ya ce an kwashe wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kura domin kula da lafiyarsu, yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka mutu a ofishin ‘yan sanda na Bebeji.

A cewarsa, “Mun samu kiran waya da misalin karfe 7:30 na safe, da samun labarin, sai muka yi gaggawar tura jami’an mu da motar mu zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto wadanda lamarin ya shafa. “Jimillar fasinjoji 45 da ke jigilar su a cikin motocin bas guda biyu ne suka yi hatsarin. Mutane 19 ne suka mutu (maza 14, manyan mata hudu da yaro namiji daya) yayin da wasu 26 suka samu munanan raunuka.

“Hatsarin ya faru ne a sakamakon gudun wuce sa’a da tukin ganganci da kuma rashin tsaro, wanda ya kai ga yin taho-mu-gama, inda motocin biyu suka kama da wuta nan take.

Mun shawarci masu ababen hawa da su guji yin gudu, wuce gona da iri da tukin ganganci,” in ji Kwamandan sashin, Mato.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here