Gwamnatin tarayya ta musanta shirin korar ma’aikata – Minista

D60A4A9A B1D8 425E A63D 93A3D65A8DF5
D60A4A9A B1D8 425E A63D 93A3D65A8DF5

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta ce babu wani shiri da gwamnatin tarayya ke yi na sallamar ma’aikatan gwamnati.

Zainab Ahmed ta bayyana haka ne a shirin ‘Barka da Safiya’ na NTA a ranar Alhamis, inda ta musanta ikirarin cewa gwamnati na shirin korar ma’aikata ne domin a samu kudi.

Ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha fadin cewa babu wani ma’aikaci da za a kore shi daga aiki.

Ministan ta ce gwamnati za ta karfafa gwiwar mutane su bar ayyukan gwamnati ta hanyar ba su kwarin gwiwa.

Ta kara da cewa, “shugaban kasa baya son korar ma’aikatan. Wannan shi ne abin da ya umarta tun farkon mulkinsa. Ya kuma umarce mu da mu biya albashi. Gwamnatin Tarayya ba ta taba gazawa wajen biyan albashi ba, ya ce dole ne mu rika biyan fansho.

Da aka tambaye ta yaya gwamnati za ta rage kudin ma’aikata, Ahmed ya ce, “To, muna fatan a karshen za a hade wasu hukumomi kuma za a rage kudin gudanar da aiki.

“Sannan kuma za mu iya samar da wasu tsare-tsare don sake horar da mutane da kuma sake tura su a wasu wuraren da suke da amfani. Misali, har yanzu muna da matukar bukatar malamai ta yadda za mu iya horar da mutane mu tura su koyarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here