
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa dakarun Amurka sun kaddamar da hare-haren sama masu ƙarfi da hallakarwa kan ’yan ta’addan kungiyar ISIS da ke aiki a arewa maso yammacin Nijeriya, tare da yin gargaɗin cewa za a ƙara kai wasu hare-hare idan har suka ci gaba da kashe Kiristoci.
Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Truth Social, inda ya ce an aiwatar da hare-haren ne bisa umarninsa kai tsaye a matsayinsa na babban kwamandan rundunonin sojin Amurka, yana mai cewa an kai farmakin ne kan mayaƙan ISIS da ake zargi da kai munanan hare-hare kan al’ummomin Kiristoci a yankin.
Ya nuna cewa hare-haren sun kasance martani ga abin da ya bayyana a matsayin kisan gilla da ake yi wa fararen hula, musamman Kiristoci, a matakai da bai taɓa ganin irinsu ba, yana mai jaddada cewa Amurka ba za ta lamunci ci gaban ta’addancin Musulunci mai tsattsauran ra’ayi ba a ƙarƙashin jagorancinsa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban Amurka ya ce tun a baya ya yi wa ’yan ta’addan gargaɗi da su daina kashe-kashe, amma suka ci gaba, abin da ya sa ma’aikatar yaƙi ta Amurka ta aiwatar da hare-haren sama da dama da ya bayyana a matsayin ingantattu ƙwarai.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun faru ne a ƙauyen Jabo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a jihar Sakkwato, inda aka kai farmakin kan wuraren da ake zargin mayaƙan ISIS ke buya.
Trump ya ƙara da yin gargaɗin cewa za a ci gaba da kai hare-hare idan har kashe-kashen suka ci gaba, tare da yabawa sojojin Amurka kan yadda suka aiwatar da aikin, yana mai cewa hakan ya nuna ƙarfin rundunar sojin ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, tsohon Twitter, sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya nuna godiya ga haɗin kai da goyon bayan gwamnatin Nijeriya, yana nuni da cewa an samu haɗin gwiwa tsakanin Amurka da hukumomin Nijeriya wajen aiwatar da hare-haren, tare da jaddada cewa kashe fararen hula a Nijeriya dole ne ya kawo ƙarshe.












































