Gwamnatin tarayya ta tabbatar da hare-haren sama na Amurka kan wuraren ’yan ta’adda a Nijeriya

Ambassador Yusuf Tuggar

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Nijeriya na ci gaba da shiga tsarin haɗin gwiwar tsaro da abokan hulɗa na ƙasashen waje, ciki har da Amurka, domin magance ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, bayan kai hare-haren sama kan wuraren ’yan ta’adda a yankin arewa maso yamma.

Ministan harkokin ƙasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana hakan ta hannun kakakin ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, Kimiebi Ebienfa, inda ya nuna cewa matakin ya samo asali ne daga ci gaba da haɗin gwiwar bayanan sirri da daidaiton dabarun tsaro da abokan hulɗa.

Ma’aikatar ta nuna cewa wannan haɗin gwiwa ya kai ga kai sahihan hare-haren sama kan muhimman wuraren ’yan ta’adda a arewa maso yammacin ƙasar, a wani yunƙuri na murkushe barazanar tsaro.

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa haɗin gwiwar na bin ƙa’idojin hulɗar ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin bangarori biyu, ciki har da musayar bayanan sirri da daidaiton dabaru, tare da girmama ikon Nijeriya da dokokin ƙasa da ƙasa.

Labari mai alaƙa: Amurka ta kaddamar da zazzafan hare-hare ta sam kan ƴan ta’addan ISIS a Nijeriya

Ta kuma bayyana cewa kare fararen hula shi ne ginshiƙin dukkan matakan yaƙi da ta’addanci, tare da kare haɗin kan ƙasa da mutunci da haƙƙin ’yan ƙasa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Gwamnatin ta sake jaddada cewa duk wani nau’in ta’addanci, ko an nufa Kiristoci ko Musulmai ko wasu al’ummomi, abin ƙi ne kuma barazana ce ga ƙimomin Nijeriya da zaman lafiyar duniya.

Ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ta nuna cewa Nijeriya na ci gaba da aiki tare da abokan hulɗa domin raunana hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda, katse hanyoyin kuɗaɗensu da jigilar kayayyaki, tare da hana barazanar ketare iyaka, yayin da ake ƙarfafa ƙarfin tsaro da bayanan sirri na ƙasa, tare da sanar da jama’a ta hanyoyin hukuma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here