‘Yan sanda sun magantu kan jerin sunayen masu zamba ta intanet da ke yawo

A0A617E4 E99F 4C1C A5CC C027B3B0582E
A0A617E4 E99F 4C1C A5CC C027B3B0582E

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta koka kan wani jerin sunaye na bogi dake yawo cewa masu damfara ne ta intanet.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, a ranar Lahadin da ta gabata ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta musanta cewa jerin sunayen da ke yawo a shafukan sada zumunta ba daga rundunar ‘yan sandan jihar ya fito ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Jerin ya kunshi mutane 31 da ake zargin an zabo daga Sagamu, Ago-Iwoye, Ijebu, da Abeokuta, kuma wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Yahya Wakilu ya sanya wa hannu.

‘’Hukumar ta ce rundunar tana zargin cewa watakila an yi amfani da jerin sunayen ne wajen karbar kudaden jama’a, don haka akwai bukatar a fadakar da jama’a cewa ba daga hannun jami’an tsaro ya fito ba.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar ba ta da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai suna Yahaya Wakilu da ya sanya hannu a cikin jerin jabun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here