Ku bi umarnin hukuncin kotun koli, ku mika kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye gare su – Tinubu ya shaida gwamnonin jihohi

Bola Tinubu scaled 1 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umurci gwamnonin jihohi 36 da su mika kuɗaɗen da ake ware wa ƙananan hukumomi kai tsaye zuwa ga ƙananan hukumomin, domin bin hukuncin kotun koli da ta yanke kan batun ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa ba za a samu cikakken ’yancin ƙananan hukumomi ba matuƙar ba a samar musu da kuɗaɗen aiwatar da ayyukansu kai tsaye ba, don haka gwamnati za ta tabbatar an bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu ba tare da tsaiko ba, kamar yadda hukuncin kotun koli ya tanada.

Ya bayyana hakan ne a taron manyan shugabannin APC na ƙasa karo na 14 da aka gudanar a cibiyar tarurruka ta fadar shugaban ƙasa a Abuja, inda ya kuma bayyana cewa ya ba ƙasashen Amurka da Tarayyar Turai tabbacin cewa Najeriya za ta kafa ’yan sandan jihohi domin magance matsalolin rashin tsaro.

Shugaban ƙasar ya kuma shawarci gwamnonin jihohi da shugabannin jam’iyya da su kasance masu sassauci a harkokinsu, su riƙa sa hannu kai tsaye a abin da ke faruwa a jihohinsu har zuwa matakin ƙananan hukumomi, ciki har da yankunan karkara, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.

Karanta: Gwamnan jihar Filato Mutfwang ya koma APC

Ya ƙara da cewa hukuncin kotun koli kan ’yancin ƙananan hukumomi wajibi ne a aiwatar da shi yadda ya kamaata, ta yadda shugabanni za su ɗauki nauyin jagoranci da muhimmanci domin ƙarfafa dimokiraɗiyya da ci gaban ƙasa.

Shugaban ƙasar ya kuma jajanta wa gwamnatin jihar Bayelsa bisa rasuwar mataimakin gwamnan jihar, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa.

Haka kuma ya buƙaci a ƙara yawan mata a cikin taron manyan shugabannin jam’iyyar, tare da tanadin hanyoyin da za su ba su dama.

Tun da farko, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yabawa ci gaban karɓuwar jam’iyyar a faɗin ƙasa, yana mai danganta hakan da sauya sheƙar wasu manyan ’yan siyasa zuwa APC, da kuma ƙaddamar da tsarin rijistar mambobi domin ƙarfafa gaskiya, adana bayanai da dimokiraɗiyya a cikin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa taron ya haɗa manyan shugabanni da suka haɗa da shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, shugabannin majalisar dokoki da gwamnonin APC, domin tsara dabarun siyasa da tsare-tsare na jam’iyyar a matakin ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here