PSC ta naɗa Gumel a matsayin mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda, ta kuma ƙara wa manyan jami’ai girma

PSC

Hukumar kula da ayyukan ’yan sandan ƙasa ta amince da naɗa Mohammed Gumel a matsayin mataimakin sufeton ’yan sanda na ƙasa DIG, tare da ƙara wa wasu manyan jami’an ’yan sanda matsayi a faɗin ƙasar.

Shugaban sashen ladabi da hulɗa da jama’a na hukumar kula da ayyukan ’yan sandan ƙasa, Torty Kalu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a birnin Abuja, inda ya ce an yanke shawarar ne bayan jarabawar rubutu da tambayoyin baki masu tsauri ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Hashimu Argungu.

Kafin wannan naɗin, Mohammed Gumel shi ne mataimakin sufeton ’yan sanda AIG mai kula da shirin tsaron al’umma, bincike da tsare-tsare, inda ya riƙe muƙami kafin a ɗaga shi zuwa matsayin DIG.

Sanarwar ta bayyana cewa an ɗaga kwamishinonin ’yan sanda bakwai zuwa matsayin mataimakin sufeton ’yan sanda AIG, yayin da aka ƙara wa mataimakan kwamishinonin ’yan sanda 13 matsayi zuwa kwamishinonin ’yan sanda.

Sabbin AIG da aka naɗa sun haɗa da Ihebom Chukwuma, Maxwell Olatokunbo, Abaniwonda Olufemi, Alonyenu Idu, Lawal Ayodeji, Agene Emmanuel da Vungmoh Kwaimo, yayin da aka kuma ƙara wa jami’an 13 girma zuwa CP da suka haɗa da Babalola Johnson, Ali Fage, Cyril Obiozo, Adepegba Adetoye, Tabitha Bako, Ofem Arikpo, Edwin Ogbeghagha, Audu Bosso, Samuel Gimba, Alhaji Danladi, Richard Gara, Lasisi Titilola da John Obiuagbaka.

Haka kuma, hukumar ta amince da ƙara wa mataimakan kwamishinonin ’yan sanda 30 girma zuwa CP, tare da ɗaga manyan sufurtendan ’yan sanda 51 zuwa mataimakan kwamishinoni, da kuma ƙara wa sufurtendan ’yan sanda 542 matsayi zuwa manyan sufintendan, yayin da aka kuma ƙara wa mataimakan sufurtendan 119 girma zuwa sufurtendan da kuma mataimakan sufurtendan 12 zuwa mataimakan sufurtendan DSP.

Shugaban hukumar kula da ayyukan ’yan sandan ƙasa, Hashimu Argungu, ya taya sabbin jami’an murna, inda ya jaddada cewa ƙarin girma na zuwa ne da ƙarin nauyi da tsammani, tare da buƙatar su ƙara jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da tabbatar da doka da oda a ƙasar nan.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here