Gwamna Yusuf ya ba da umarnin biyan duk basussukan EAA ga ma’aikatan jami’a mallakin jiha

WhatsApp Image 2025 12 18 at 23.19.04 750x430

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa za a biya dukkan basussukan alawus-alawus na ilimi da aka samu na EAA da ma’aikatan jami’a mallakin gwamnatin jiha ke bi kafin ƙarshen watan Disamba na shekarar 2025.

Haka kuma, gwamnan ya ba Kwamishinan filaye da tsara muhalli umarnin tantance dukkan filayen Jami’ar Northwest Kano, tare da soke duk wani rabon fili ba bisa ƙa’ida ba ko mamaye fili da gwamnatin da ta gabata ta yi.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa gwamnan ya faɗi hakan ne a zaman majalisar zartarwa ta jiha karo na 35.

Gwamnan ya yi jawabin ne a lokacin da Shugaban majalisar jami’ar Northwest Kano ya jagoranci mambobin majalisar da shugabannin jami’ar a wata ziyarar girmamawa, domin gabatar da Farfesa Amina Salihi Bayero a hukumance a matsayin sabuwar shugabar jami’a.

Karin labari: Gwamnan Kano ya jaddada rashin lamuncewar sa da ayyukan rashawa, ya nemi matasa su shiga yaki da cin Hanci

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Farfesa Bayero ita ce shugabar jami’a mace ta farko a tarihin jami’ar, kuma ta taso ne daga cikin ma’aikatan farko na ilimi da suka kafa jami’ar.

A cewar sanarwar, gwamnan ya yaba wa majalisar gudanarwar jami’ar bisa naɗa cikakkiyar shugabar jami’a bayan tsari mai tsawo, nagarta da bayyana gaskiya.

Ya kuma buƙaci sabuwar shugabar jami’ar da ta gudanar da aikinta da ƙwazo, tare da haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki domin inganta darajar ilimi a tsawon wa’adin mulkinta na shekaru biyar.

Gwamna Yusuf ya tabbatar wa sabuwar shugabancin jami’ar cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da ɗaukar matakan magance ƙalubalen da ke fuskantar jami’ar, tare da nuna fata na samun ingantaccen matakin ilimi da bunƙasar cibiyar a ƙarƙashin sabon jagoranci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here