A ranar Asabar ne mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya halarci daurin auren Mustapha Sani Abacha, dan tsohon shugaban kasa, da Safa Tijjani Saleh Geidam.
Daurin auren ya gudana ne a masallacin Mohammed Ali, tsohuwar GRA dake Maiduguri a jihar Borno.
Karanta wannan: Malamai 3 ne kacal a Makarantar Sakandiren yaran mu Mata-Iyaye a Sumaila
Daga cikin muhimman mutanen da suka halarci taron akwai Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, da sauran manyan baki.
Ga hotunan daurin auren: