Jam’iyyar PDP ta ayyana Alhaji Mustafa Sule Lamido, dan tsohon gwamnan Jigawa, a matsayin wanda ya samu tikitin jam’iyyar na takarar kujerar gwamna a 2027.
Babban jami’an ayyana sakamako da tabbatar da dan takara a zaben fidda gwani, Mista Isa Ahmed, ne jagoranci zaben fidda gwani da aka gudanar a Dutse, inda ya tabbatar da Mustapha Sule Lamido a matsayin dan takara daya tilo a ranar Lahadi, ya ce nasarar ta yi daidai da kundin tsarin mulki da ka’idojin jam’iyyar.
Lamido, wanda shi ne kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar a 2023, ya gode wa shugabannin jam’iyyar kan yadda suka gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana a fadin jihar.
Ya taya sauran ‘yan takarar PDP a jihar murna, sannan ya yi alkawarin inganta hadin kai a cikin jam’iyyar.
Ya bayyana ci gaban tattalin arziki, karfafa matasa, ilimi, lafiya, farfado da al’umma, da gyaran cibiyoyi a matsayin muhimman abubuwan da zai mayar da hankali a kai idan aka zabe shi.
“Wannan lokaci ba sabo ba ne a gare ni, a 2023 kun ba ni wannan dama, kuma tare muka gudanar da yakin neman zabe da ya dogara kan hadin kai, fata, gyara, da alkawarin samar mafi kyawun Jigawa.
“Ko da yake ba mu samu nasara ba a lokacin, amma mun samu amincewar daruruwan dubban mutanenmu, sannan muka kafa tushe mai karfi.
“Yau mun koma fagen takara ne saboda matsaloli da kalubalen da ke addabar jihar mu mai albarka har yanzu suna nan,” inji shi.












































