FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari’a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama 

Minister of Education Mallam Adamu Adamu
Minister of Education Mallam Adamu Adamu

Kotun masana’antu a ranar Litinin ta dage sauararon sharia’a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.

Mai shari’a Polycarp Hamman ya dage sauraron shari’ar ne saboda a bai wa gwamnatin tarayya mika dukkan takardun da suka dace don karar.

Gwamnatin tarayya ta garzaya gaban kotun masa’antu ta kasa dake zama a Abuja inda take bukatar a umarci kungiyar malamai masu koyarwa ta jami’o’i, ASUU, da su koma bakin aikinsu a yayin da ake kokarin shawo kan rashin jituwar dake tsakaninsu.

A wata takardar da shugaban yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da aikin yi, Olajide Oshundun ya fitar, yace a ranar 8 ga watan Satumba ne ministan kwadago ya aike da lamarin gaban magatakardan kotun masana’antu.

ASUU ta fada yajin aikin sati hudu a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma ta cigaba duk da tattaunawar da take da gwamnatin ba a samun wata matsaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here