Wani lamari ya faru a daren Talata a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, inda kayan aikin kasa da kamfanin kula da sufurin jiragen sama na NAHCO da ake amfani da su suka lalata wani jirgin kamfanin Air Peace.
Sakamakon haka, da yawa daga cikin shirye-shiryen zirga-zirgar jiragen sama na iya fuskantar jinkiri, sannan ana iya soke wasu yayin da kamfanin jirgin ke daidaita ayyukansa don rage tasirin wannan tsaiko.
Air Peace ya tabbatar da cewa an lalata daya daga cikin jiragen sa samfurin Airbus A320 a kasa a ranar 14 ga Yuli 2026, bayan da wata motar kwashe kaya ta NAHCO ta yi karo da injin jirgin, jim kadan bayan ya kammala saukar P47427 daga Kano kuma fasinjoji sun sauka lafiya.
SolaceBase ya rawaito cewa an taba samun tsaiko a zirga-zirgar jirgin Air Peace samfurin Embraer 195-E2 da aka sayo sabo a ranar Jumma’a, 26 ga Disamba 2025, biyo bayan wani lamari na kula da zirga-zirga a kasa a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Air Peace ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan fasinjoji sun riga sun shiga jirgin, lokacin da wata motar kwashe kaya mallakar NAHCO ta yi karo da daya daga cikin injunan jirgin.
A cewar Air Peace, jirgin mai lambar 5N-BYH, an tsara zai yi wa jirki mai lamba P47750 ne daga Legas zuwa Accra a lokacin da lamarin ya faru.
A cikin wata sanarwa da kamfanin Air Peace ya fitar a safiyar ranar Laraba, kamfanin ya bayyana cewa “Kayan aikin kasa na kamfanin NAHCO sun tsaga jirgin, kuma hakan ya sa jirgin ya daina aiki gaba daya.”











































