Majalisar wakilan Najeriya na zargin ma’aikatar mata da boye Naira Biliyan 1.5

Majalisar, Wakilan, Najeriya, zargin, ma’aikatar, mata, boye, Naira, Biliyan
Majalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da bincike kan Naira biliyan 1.5 da aka ware domin biyan ‘yan kwangila, amma ana zargin manyan jami’an ma’aikatar mata...

Majalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da bincike kan Naira biliyan 1.5 da aka ware domin biyan ‘yan kwangila, amma ana zargin manyan jami’an ma’aikatar mata ta tarayya sun karkatar da makudan kudaden.

Kwamitin majalisar mai kula da harkokin mata ya fara gudanar da bincike a Abuja kan korafe-korafen da ‘yan kwangila suka yi kan rashin biyan kwangilolin da aka aiwatar.

Shugaban kwamitin Kafilat Ogbara, ya bayyana cewa ma’aikatar ta bullo da sabbin kwangiloli da ba a kama su a cikin kasafin kudin 2023 ba tare da karkatar da Naira biliyan 1.5 a matsayin kudaden tsofaffin ‘yan kwangila.

Karin labari: Kotu a Abuja ta umarci NCoS ta bayyana takardar shaidar lafiyar jami’in Binance

Ta kara da cewa ma’aikatar, yayin da take bin ‘yan kwangila, ta ba da sabbin kwangiloli a jihohi 15 na tarayya, wanda ta yi zargin ba a kama su a cikin kasafin kudin 2023 ba.

A cewarta, “ba a biya kudin ‘yan kwangila ba, an karkatar da kudi, to ta yaya kuke biyan wadannan ‘yan kwangilar”?

Ta ce akwai ci gaba da binciken ma’aikatar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta yi kan fitar da kudaden da aka kashe a watan Nuwamba da Disambar 2023 zuwa Naira biliyan 1.5.

Karin labari: CBN ya bayyana sanyawa bankunan ajiyar kudi takunkumi

Wadanda suka shigar da karar, a cewar Ogbara sun kuma yi zargin cewa ma’aikatar ta sayi ababen hawa a barikin soji da ke Abuja.

Mista Aloy Ifeakandu, Daraktan Kudi da Gudanarwa a ma’aikatar, ya ce ya bi umarnin hukuma ne kawai daga manyansa, yana mai cewa bayanan suna nan.

NAN ta rawaito cewa ofishin Akanta Janar na kasa ya bayyana cewa an saki Naira biliyan 1.5 ga ma’aikatar.

Karin labari: An bawa Najeriya bakuncin bankin makamashi na dala biliyan 5 na Afirka

A halin da ake ciki, kwamitin ya gayyaci ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye da ya gurfana a gaban sa a ranar Talata, 9 ga watan Yuli.

Kwamitin ya kuma umurci ma’aikatar da ta dakatar da duk wasu ayyukan kwangila a shekarar 2024, “har sai an warware matsalar tare da neman a ba ‘yan matan Chibok asusu na musamman da kuma yarjejeniyar fahimtar juna kamar yadda NAN ta tabbatar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here