Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da ayyukan jirage masu zaman kansu guda goma bisa gaza fara aikin sake tantancewa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Michael Achimugu, Daraktan Hulda da Jama’a da Kare Kayayyakin ciniki a ranar Juma’a a Abuja.
Hukumar ta ce dokar zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya mai lamba 2023 sashe na 18.3.4 ta haramtawa masu izinin zirga-zirgar jiragen sama da ba na kasuwanci ba (PNCF) yin amfani da jirginsu wajen jigilar fasinja.
Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya na zargin ma’aikatar mata da boye Naira Biliyan 1.5
“Sakamakon rashin mutunta wannan doka, a baya NCAA ta umarci duk masu rike da PNCF da su sake tantancewa wanda yakamata a kammala a ranar 19 ga watan Afrilu, 2024.
“Don haka, NCAA ta dakatar da PNCF daga gudanar da ayyukanta.
“An sanar da jama’a cewa ba bisa ka’ida ba ne a shigar da masu rike da PNCF don kasuwanci. Hukumar ta NCAA ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fara aiwatar da ayyukan tilastawa duk wani mai rike da PNCF da aka samu da laifin aikata ba bisa ka’ida ba,” in ji hukumar.
Hukumar ta ce an tura jami’anta zuwa tashar jiragen sama masu zaman kansu domin sanya ido kan ayyukan masu rike da PNCF kamar yadda NAN ta bayyana.