
A kasa da jihohi 10 ciki harda babban birnin tarayya, Abuja, ko dai sun fuskanci ambaliyar ruwa ko kuma an sami asarar rayuka yayin da ruwan sama ya tsananta a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
A cewar ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Farfesa Joseph Utsev, wanda ya yi watsi da gargadin yayin ganawa da manema labarai a Abuja, wasu jihohi 21 na iya fuskantar ambaliyar ruwa.
Idan ba’a manta ba a ranar Larabar da ta gabata an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Legas da Ogun.
Karin labari: Hukumar NCAA ta dakatar da jirage 10 masu zaman kansu
Ambaliyar ruwan ya ruguza wani bene mai hawa biyu a unguwar Mushin da ke Legas tare da mamaye mazauna yankin yayin da dalibai suka kasa zuwa makarantu a sassan jihar.
Haka zalika, ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da wani almajiri a unguwar Ketu da ke Legas.
Utsev ya bayyana cewa, rahoton ambaliyar ruwa na shekara-shekara da Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya ta fitar a watan Afrilu ya yi hasashen cewa kananan hukumomi 148 a cikin jihohi 31 sun fada cikin yankunan da ake fama da matsalar ambaliya.
Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya na zargin ma’aikatar mata da boye Naira Biliyan 1.5
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina da kuma Kebbi.
Sauran sun hada da Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Ribas, Sokoto, Taraba da kuma Yobe.
Ministan ya yi gargadin cewa kwalara na iya kara yaduwa a Najeriya sakamakon ambaliyar ruwa.
Karin labari: Kotu a Abuja ta umarci NCoS ta bayyana takardar shaidar lafiyar jami’in Binance
Ya kuma kara da cewa za’a fara ambaliya kogi a wannan watan, kuma za’a samu a jihohin Ondo, Kaduna, Anambra, Benue, Adamawa da sauran jihohi 12.
Ministan ya yi nuni da cewa Najeriya tana cikin kogin Neja wanda wasu kasashe takwas suka mamaye da suka hada da Benin da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Cote D’Ivoire da Guinea da Mali da kuma Nijar.












































