Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro kan su gaggauta kubutar da duk wadanda masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a fadin kasar nan.
Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno, shi ne ya bayyana hakan inda ya ce shugaba Buhari ya bayar da umarnin ne a taron tattaunawa na majalisar tsaro ta kasa na shekarar 2022, wanda shugaban kasar ya jagoranta a fadarsa ta Villa dake Abuja.
Ya bayyana cewa shugaban ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane ke ci gaba da kashe mutane a kasar nan.
“Shugaban ya bayyana bacin ransa dangane da kalubalen tsaro da ake ci gaba da samu a kasar, musamman lamarin da ya faru har yakai ga ‘yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu tare da kama wasu da dama.
“Ba kawai wadanda aka kama a cikin jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ba amma har da wadanda aka yi garkuwa da su a wasu sassan kasar nan.
“Shugaban kasa ya umurci dukkan jami’an tsaro da jami’an leken asiri da su kubutar da duk wadanda ba su ji ba ba su gani ba cikin gaggawa ba tare da sun ji rauni ba.
“Babban Hafsan hafsoshin tsaro da Hafsoshin Soja da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda duk sun yiwa shugaban kasa bayanin abubuwan da ke faruwa a hukumominsu.”
Ya bayyana cewa ya bayar da wasu shawarwari kan yadda za a magance kalubalen tsaro da ke addabar al’umma.
A cewar Monguno, ana daukar kwararan matakai domin tabbatar da tsaron dukkan iyakokin kasar, da nufin magance kalubalen tsaro da ka iya tasowa daga yankunan da lamarin ya shafa.
Ya ce a yanzu barazanar ta bar yankin Arewa maso Gabashin kasar nan koma yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya, amma dole a dakile hakan.













































