Gwamnatin Plateau ta fara binciken zargin kashe shanu 36 da guba

Caleb Mutfwang

Gwamnatin jihar Filato ta fara gudanar da bincike kan zargin sa guba da aka yi wa shanu a unguwar Tafi Gana da ke karamar hukumar Bassa ta jihar.

Misis Joyce Ramnap, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Jos.

Ramnap ta ce matakin ya zama wajibi domin kwantar da tarzoma tare da dakile barazanar tsaro da ake fuskanta a garin Bassa da kewaye.

“An ja hankalinmu kan wani zarge-zargen da ke yawo a shafukan sada zumunta, dangane da zargin kashe wasu shanu 36 na wani Malam Samaila Nuhu da ke unguwar Tafi Gana a garin Bassa ya yi.

Karin karatu: Ta’addanci: An sake kashe mutane 40 a wani sabon harin da aka kai Filato

“An riga an tura tawagar kwararrun likitocin dabbobi, jami’an kula da muhalli, da masu bincike don tattara samfuri da kuma gano gaskiyar lamarin da ake zargin guba ne,” in ji ta.

Ramnap ta bayyana kudurin gwamnati na inganta zamantakewa cikin lumana, har ma ta gargadi mazauna garin da su daina yin kalamai masu tayar da hankali tare da ba da damar bin ka’ida wajen gudanar da bincike. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here