Mutane 40 ne suka mutu a wani harin da wasu mahara suka kai kan al’ummar Zike, Kimakpa da ke gundumar Kwall a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
A cewar wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, maharan sun mamaye kauyen ne da sanyin safiyar Litinin din nan inda suka yi ta harbe-harbe kan mazauna kauyen da ke tururuwa domin tsira bayan sun ji karar harbe-harbe.
Shugaban al’ummar ya shaidawa gidan Talabijin na Channels ta wayar tarho cewa tawagar ‘yan banga da suka hada da shi da wasu jami’an tsaro suna sintiri a wata unguwa lokacin da maharan suka mamaye kauyen suka fara harbe-harbe.
Ko da yake jami’an tsaro sun yi artabu da maharan tare da samun nasarar dakile su, sai dai an yi barna, inda aka harbe kimanin mutane talatin da shida, wasu hudu kuma suka mutu daga baya.
Wasu mazauna garin sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga kuma suna samun kulawar likitoci a asibiti.
Har yanzu dai hukumomin tsaro a jihar ba su ce uffan ba kan harin da ke zuwa cikin kasa da makonni biyu bayan an kashe mutane hamsin da biyu a wasu al’umomin karamar hukumar Bokkos da ke jihar Arewa ta tsakiya.
Jihar Filato dai ta shafe shekaru da dama tana fama da kashe-kashe, inda ‘yan bindiga suka kori daukacin al’umma.