NPFL: Kano Pollers ta doke Lobi Stars da ci 2-0

Kano Pillars 700x430

Kungiyar kwallon kafa Kano Pillars ta doke Lobi Stars dake garin Makurdi da ci 2-0 a gasar cin kofin Premier ta kasa.

Wasan ya kasan ce na mako 33, ne a ci gaba da gasar wanda aka gudanar dashi a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata a jihar Kano.

An buga wasan ne a ranar Lahadi 13 ga watan Afrilun shekarar 2025 a gasar Premier ta shekarar 2024/2025

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagle Ahmed Musa ne ya fara zura kwallo a mintuna na 55 da fara wasan.

Yayin da daga bisani Naziru Ibrahim ya kara kwallo ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Nasarar da Pillars’ ta samu ya sanya ta kara matsawa a matsayin da take na jerin jadawalin kungiyoyin dake buga gasar.

Bayan tashi daga wasan mai horar da yan wasan na Kano Pollers Usman Abdallah ya yaba da kwazon yan wasan nasa tare kuma da jinjina musu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here