Kotun Koli ta yi watsi da ƙarar shugaba Buhari da Malami kan dokar zaɓe

supreme court
supreme court

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, suka shigar inda suka buƙaci a share sashi na 84 (12) na sabon kundin zaɓe 2022.

Yayin yanke hukunci ranar Jumu’a, kwamitin Alƙalai Bakwai bisa jagorancin Mai Shari’a Musa Dattijo Mohammed, sun cimma matsaya guda cewa Buhari, kasancewar da shi aka yi dokar ya rattaɓa hannu a kai, ba zai dawo yana yaƙar wani sashi ba. Kotun bayan ta karbi bayanan majalisar tarayya da sauran waɗan da ake ƙara, ta bayyana cewa Kotun Ƙoli ba ta hurumin sauraron lamarin kuma ƙarar cin mutunci ne ga tsarin Kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here