Hukumomin tsaro a Najeriya sun kaddamar fa farautar ’yan siyasar da ake zargi da yunkurin kawo cikas ga rantsar da shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu da mataikainsa, Kashim Shettima, a ranar 29 ga watan Mayu.
Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya sanar a safiyar Litinin a Hedikwatar rundunar cewa suna gudanar da aikin ne da hadin gwiwar hukumomin leken asiri da sauran hukumomin tsaro.
Ya ce yin hakan na muhimmanci domin dakile masu neman tayar da zaune tsaye a Najeriya.
“Mun lura bayan zaben shugaban kasa, wasu ’yan siyasa da sakamakon bai yi musu dadi na ta barazana da nufin tayar da fitina domin hana rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.
“Rundunar ’yan sanda na gargadin duk ’yan siyasa da yaransu da kuma abokansu masu irin wannan manufa da su shiga hankalinsu a yunkurin da suke na kawo wa bikin ranar 29 ga wata cikas.”
(Aminya)













































