Wasu matasa sun kashe mahaifiyar su ya yin da take kokarin rabasu fada a Abuja

Police olopa
Police olopa
Sai dai har yanzu bamu samu bayani kan abunda ya hada ragimar ba, amma mun sami rahotan cewa ‘ya ‘yan Zainab sun sari mahaifiyar ta su ne da adda bisa kusrkure ya yin da suke tsaka da ragima.
Lamarin ya faru ne a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar a unguwar Kpaduma II dake Asokoro.
Wani mazaunin unguwar da lamarin ya faru, mai suna Saliu Shehu, ya ce an garzaya da Zainab asibiti kafin ta ce ga garinku nan.
“Matasan da suke fadan uwar su daya uban su daya, mahaifiyar tasu tayi kokarin ta raba su ya yin da suke tsaka da fada, Inda Inusa ya zunduma da gudu ya dauko adda da niyar ya sari dan uwansa da ita, garain kokarin kai sara ya sari babar sa, ya yin da abun ya faru an dauke ta zuwa asibiti rai a hannun allah kafin ta rasu.” Inji Saliu Shehu.

Ya yin da muka tun-tun tube kakakin hukumar yan sandan babban birnin tarayya abuja, Josephine Adeh, ya ce suna neman Inuwa ruwa a jallo.

Adeh ya ce “Mun sami labarin faruwa lamarin inda ba tare da bata lokaci ba muka je inda abin ya faru, an dau mahaifiyar tasu zuwa asibiti kafin ta rasu a cen. a halin yanzu muna tsare da usaman yayin da shikuma Inusa ya tsere, amma munan mun baza jami’an tsaron domin kamoshi a duk inda yake.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here