Bayan fiye da shekara ɗaya da SolaceBase ta fallasa halin da makarantar Firamare ta Faradaci da ke ƙaramar hukumar Sumaila ta jihar Kano ke ciki, a ƙarshe dai an gyara makarantar.
Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan wani rahoto da aka samu kan makarantar.
Ajujuwan makarantar wadda ke da ɗalibai fiye da 500, sun kusa rugujewa lamarin da ya sanya aka haɗe su a Ajujuwa 2.
Gyaran ya biyo bayan labarin da SolaceBase ta wallafa a watan Mayun shekerar 2024 da kuma wani rahoton da ya biyo baya a ranar 11 ga Mayun shekerar nan da muke ciki ta 2025, wanda ya yi cikakken bayani game da yanayin rashin tsaro da rashin kula da makarantar ke ciki, wanda ya jawo hankalin kafofin yaɗa labarai dangane da koken jama’ar yankin.
Rahoton ya sa gwamnatin jihar Kano ta amince da gyaran makarantar.
Kansila mai wakiltan Garfa, Gaddafi Yusuf Yunusa ne ya gudanar da aikin gyare-gyaren tare da goyon bayan gwamnatin jihar da kuma kulawa.
Da yake magana da SolaceBase a ranar Juma’a, Kansilan, ya tabbatar da gyaran.
“Alhamdulillah gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da yin gyaran, mun zabi Faradaci ne saboda yanayin da ta ke ciki ya fi na sauran makarantun yankin.” Inji shi.

“Ya zuwa yanzu mun gyara daya daga cikin gine-gine biyu da ba su da da kyau, shugaban karamar hukumar mu ya yi alƙawarin gyara sauran nan ba da daɗewa ba a matakin karamar hukumar.”

Wasu mazauna yankin, sun yaba da ƙoƙari da gudunmawar Solacebase kan wannan gyara.
Wani mazaunin garin Malam Mu’aruf Galadima shi ma ya tabbatar wa wakilinmu gyaran.













































