Kungiyar Malaman Jami’o’i reshen Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ta yi barazanar fara shirin janye takardar shaidar digiri na Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa, Kashifu Inuwa, a matsayin tsohon dalibin jami’ar.
Kungiyar ta ce, an yi la’akari da wannan janyewar ne bayan da Inuwa ya gabatar da cewa, tsarin da Kungiyar ta fito da shi na biyan albashi wato UTAS ya gaza samun nasara a gwajin inganci, gwajin raunin da gwajin amincin tsaro da aka yi masa.
ASUU ta bayyana jawabin nasa, wanda ta yi ikirarin cewa, an gabatar da shi ne a ranar 9 ga Maris, 2022, bayan taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya, a sakamakon jagorancin maigidansa, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki da fasahar zamani, Isa Pantami a matsayin zance mara tushe balle makama.
Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis mai taken: KARYA UTAS DA NITDA, wadda shugaban kungiyar ASUU reshen ATBU, Ibrahim Inuwa ya karanta wa manema labarai, kungiyar ta shawarci shugaban NITDA da ya koma kan tafarkin gaskiya da kuma daukakar ilimi.
“Ba mu yi mamakin yunƙurin da jami’an gwamnati suka yi ba musamman Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki da fasahar zamani da DG, NITDA na kashe UTAS,” in ji kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Dukkansu sun nuna matsananciyar rashin kishin kasa a cikin mu’amalarsu da kuma magance matsalolin da suka shafi ofisoshinsu da mukamansu a gwamnati, inda suka nuna rashin isassun kayan aiki da halin da Jami’o’in gwamnati ke ciki a Najeriya.
‘’Ya kamata Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki ya iya raba alhakinsa na hukuma da bukatunsa na kashin kai.
Fatanmu shi ne babu wani yunkuri da Ministan da mukarrabansa za su yi na kawo cikas ga tsarin UTAS saboda tsayuwar da ASUUS ta dauka a kan gazawar da jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Owerri ta yi na nadinsa Farfesa a matsayin Farfesa na Jami’ar.”
“An bukaci shugaban NITDA da ya koma kan turbar gaskiya da daukakar ilimi da Jami’ar ta ba shi digiri, wanda gazawarsa wajen yin hakan zai sa a kwace digirinsa a matsayin tsohon dalibin ATBU, Bauchi.”













































