Hukumar Kwastam ta dakatar da horar da sababbin jami’ai 3,852 saboda damawar da FCC ta nuna

BASHIR ADEWALE ADENIYI Customs 750x430

Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa (NCS) ta dakatar da horar da sababbin jami’ai 3,852 da ta dauka aiki, kusan shekaru biyu bayan fara aikin daukar ma’aikatan, sakamakon damuwar da Hukumar Kula da Daidaito a Rabon Ayyukan Gwamnati (FCC) ta nuna kan zargin samun matsaloli a zaɓin da gayyatar wadanda suka yi nasara.

Dakatarwar, wacce aka sanar a ranar Juma’a cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwanturolan Kwastam kuma mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Maiwada, ya sanya wa hannu, ta biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabancin hukumar Kwastam da tawagar FCC, inda hukumomin biyu suka amince da ci gaba da shawarwari domin warware sabanin da ke tsakaninsu.

Sanarwar ta ce, “Hukumar Kwastam ta Najeriya ta dakatar da ayyukan horarwa da ake gudanarwa a kwalejojin horarwarta guda biyu na wucin gadi, domin ba da damar ci gaba da shawarwari da tattaunawa da Hukumar Kula da Daidaito a Rabon Ayyukan Gwamnati (FCC), kan warware matsalolin da aka gabatar dangane da aikin daukar ma’aikata da ake yi.

“Matakin ya biyo bayan tattaunawa tsakanin hukumar da tawagar NCS, inda bangarorin biyu suka sake tabbatar da kudurinsu na warware matsalolin ta hanyar tattaunawa mai ma’ana, fahimtar juna da kuma ci gaba da hadin gwiwa tsakanin hukumomi.”

Maiwada ya ce hukumar ta dakatar da horar da ma’aikata a kwalejojin horarwarta biyu sakamakon damuwar da FCC ta nuna kan aikin daukar ma’aikatan.

Ya ce dakatarwar na da nufin ba wa hukumomin biyu damar warware sabanin da ke tattare da aikin daukar ma’aikatan ta hanyar karin shawarwari da tattaunawa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta tambayoyi kan yadda aka zabi wadanda suka yi nasara, bayan wasu masu neman aikin sun yi zargin an cire su daga cikin wadanda aka gayyata zuwa horo, duk da cewa sun ga sunayensu a jerin sunayen karshe da hukumar ta wallafa.

Hukumar ta ce hukumomin biyu sun sake tabbatar da kudurinsu na warware matsalolin ta hanyar tattaunawa mai ma’ana, fahimtar juna da ci gaba da hadin gwiwar hukumomi.

Ta bayyana cewa Kwanturola Janar na Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya sake jaddada kudurin hukumar na yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati domin amfanin kasa.

“Bisa la’akari da damuwar da hukumar ta nuna da kuma jerin tattaunawar da aka gudanar, Kwanturola Janar na Kwastam, CGC Bashir Adewale Adeniyi, MFR, ya sake tabbatar da kudurin hukumar na hadin gwiwa da sauran hukumomin gwamnati da kuma tattaunawa mai ma’ana, domin da zata amfani kasa baki daya.

Hukumar Kwastam ta kara da cewa tana daraja dadadden alakar da ke tsakaninta da FCC, kuma tana da yakinin cewa tattaunawar da ake yi za ta ba da damar warware matsalolin da aka gabatar.

Hukumar ta kuma yi alkawarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a dukkan matakan da ake bi, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da tuntubar hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin kara karfafa amincewar jama’a da ayyukanta

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here