Sufeto-Janar na ‘yan sanda, (IGP) Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan turmutsitsin da ya faru a Oyo, Anambra, da kuma babban birnin tarayya.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Egbetokun ya gargadi masu shirya taron cewa sakaci a bangarensu laifi ne.
IGP din ya ce “rashin ingantaccen tsari” na rabon kayan jin dadin rayuwa a karamar hukumar ya haifar da rudani da rigima da ba dole ba.
Egbetokun ya roki kwamishinonin ‘yan sanda a jihohin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike kan wadannan munanan al’amura domin ci gaba da shari’a.