Uwargidan shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu, ta karyata jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta da sauran kafafen yada labarai, wanda ke nuni da cewa ta shirya wani taron addu’o’i na kasa.
Ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin.
Wani rahoto ya yi ikirarin cewa Mrs Tinubu da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, za su jagoranci taron na kwanaki bakwai domin yiwa kasa addua.