Shugaba Bola Tinubu ya amince da sake nada Farfesa Abdullahi Mustapha a matsayin Darakta Janar na Hukumar Bincike da Bunkasa Fasaha ta Kasa (NBRDA), na tsawon shekaru biyar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na NBRDA D-G, Toyin Omozuwa ya fitar a Abuja ranar Asabar.
A cewar sanarwar, an mika nadin Mustapha ne a wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren gwamnati (SGF), Sen. George Akume.