CISLAC ta danganta matsalar yunwa, mutuwar al’umma da rashin kyakkyawan mulki a Najeriya

images (17)

 

Cibiyar CISLAC ta nuna damuwa kan matsalar yunwa da ke kara ta’azzara a Najeriya, wacce ke haifar da turmutsutsu a wuraren rabon kayan agaji wasu lokutan hadda rasa rayuka.

Shugaban CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce wannan matsala tana nuna yadda rashin kyakkyawan mulki da gazawar gwamnati wajen yaki da talauci suka shafi rayuwar ‘yan Najeriya.

A Abuja, turmutsutsu a wurin rabon kayan agaji a coci ya yi sanadin mutuwar mutane goma, ciki har da yara hudu.

Haka kuma a Okija, jihar Anambra, rabon shinkafa ya yi sanadin mutuwar mutane 12, tare da jikkata wasu 30.

Rafsanjani ya ce gwamnatin Tinubu da sauran hukumomi ya kamata su mayar da hankali kan tsaro, bunkasa noma, da samar da ayyukan yi don rage yunwa da talauci.

Ya kuma bukaci kyakkyawan tsari a rabon kayan agaji don guje wa rasa rayuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here