Gwamnatin Kano za ta hukunta marasa biyan haraji, ta shirya tara biliyan N80 a 2025  

Abba Kabir Yusuf sabo 1

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin fara gurfanar da masu kaucewa biyan haraji daga shekarar 2025 a matsayin wani bangare na sabbin gyare-gyare don inganta harkar karbar haraji da tabbatar da biyayya ga dokoki.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Asabar a Kaduna.

Shugaban Hukumar Tattara Kudaden Shiga na Jihar Kano (KIRS), Dr. Zaid Abubakar, ya bayyana hakan yayin gabatar da jawabi ga Gwamnan a wurin Taron Bita na Manyan Jami’an Gwamnati.

A cewar sanarwar, gyare-gyaren ba don kara yawan haraji aka yi ba, sai don inganta hanyoyin karba da tabbatar da mutane na bin dokokin haraji.

Dr. Abubakar ya kara da cewa, ana sa ran jihar za ta iya tara fiye da naira biliyan ashirin duk bayan wata uku a shekarar 2025, wanda zai kai jimillar sama da naira biliyan tamanin a shekara.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, karkashin jagorancin Gwamna Yusuf, an sake fasalin hukumar KIRS, wanda hakan ya haifar da sakamako mai kyau a zangon karshe na shekarar 2024.

Shawarar Gwamnan na sauya shugabancin hukumar da kafa sabon tsarin gudanarwa ya taimaka matuka wajen inganta ayyukan hukumar.

Bugu da kari, za a kaddamar da sabon tsari na tattara haraji a shekarar 2025.

Wannan sabon tsarin na da nufin kara yawan kudaden shiga da kuma tallafawa kokarin gwamnati na cika alkawuran zabe a bangarorin ci gaba daban-daban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here