Kungiyar kare hakkin dan Adam ta SEDSAC ta jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan nadin ‘yan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama guda biyu a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwa ta Jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da Daraktan SEDSAC, Comrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana nadin Ambasada Ibrahim Waiya da Comrade Nura Iro Ma’aji a matsayin abin yabo da nuna kyakkyawar fahimtar siyasa don ciyar da jihar gaba.
Sanarwar ta kara da cewa wadanda aka nada suna da tarihin aiki a fannin kare dimokuradiyya kuma suna da kishin kawo cigaba.
Kungiyar ta kuma bukaci su hada kai da kungiyoyin farar hula don habaka cigaban Kano.
A karshe, SEDSAC ta yi fatan Allah ya ba su ikon gudanar da ayyukansu don ciyar da jihar Kano gaba a fannin tattalin arziki da siyasa.