YANZU-YANZU: Kotu ta tsige gwamnan Ebonyi da mataimakinsa daga kan mukamansu

David Umahi 1 1
David Umahi 1 1

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi da mataimakinsa da Eric Kelechi Igwe da su gaggauta ficewa daga ofishinsu bayan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani hukunci da ya yanke a ranar Talata, ya bayyana cewa bayan ficewa daga jam’iyyar da suka lashe zaben, Umahi da Igwe dole sai sun yi murabus daga ofishinsu.

Mai shari’a Ekwo ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta karbi sunayen mutane daga hannun jam’iyyar PDP domin maye gurbin Umahi da Igwe, domin cika ragowar wa’adin mulkinsu, ko kuma ta sake gudanar da sabon zabe domin maye gurbin Umahi da Igwe.

Alkalin, ya hana Umahi da Igwe ci gaba da yin kane-kane ko nuna kansu a matsayin Gwamna da Mataimakin Gwamnan Jihar Ebonyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here