Majalisar wakilai ta kuduri aniyar sake duba kudurorin da ba su yi nasara ba domin inganta muradun mata a gyaran kundin tsarin mulkin da ake yi.
A ranar Talata, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce za a yi hakan nan da wasu makonni masu zuwa.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da dubban mata suka sake tare babbar kofar shiga majalisar dokokin kasar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin rashin adalcin da ake yi wa mata a kasar.
Matan da suka yi zanga-zangar da suka tare kofar Sakatariyar Tarayya ta Majalisar, sun yi zanga-zangar kin amincewa da kudirin dokar jinsi yayin da aka yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima a makon jiya.













































