Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’kamatis Sunnah (JIBWIS) reshen karamar Hukumar Kankia a Jihar Katsina, ta sanar da rufe Masallacin Juma’a da ke Layi Quarters, wanda ya shafe shekara 40 ana Sallah a ciki sakamakon ambaliyar ruwa.
Sheikh Khalil Kasim ne ya sanar da hakan, inda ya ce a yanzu za a gudanar da Sallar Juma’a a Masallacin Ibn Taimiyya da ke Gurara, wanda shi ne Masallacin da ake Salloli biyar.
Shugaban JIBWIS na yankin Alhaji Umaru Bature ya bayyana cewa sun cimma matsayar ne a wata ganawa da babban limamin masallacin Malam Tasiu Umar da shugaban kwamitin masallacin Malam Alkhamis Rabiu.
Ya ce an gina masallacin mai hawa daya ne a shekara ta 1985.
Karin karatu: Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu
Bature ya bayyana cewa masana sun ba da shawarar a rufe wurin ibadar saboda ruwa ne ya rutsa da shi sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu kwanan nan a garin.
Ya ce Masallacin da yake ginin bene, wanda ruwa ya rutsa da shi, yana da hadari mutane su yi salla a cikinsa a lokacin.
Don haka ya nemi gudunmuwa daga daukacin al’ummar musulmi muminai da kungiyoyi, kamfanoni daga ciki da wajen kasar nan domin sake gina shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a kwanakin baya ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da lalata kadarori da aka kiyasta sun kai biliyoyin Naira.
NAN ta tattaro cewa wannan ne karon farko cikin shekaru arba’in da suka gabata a tarihin garin, da aka fuskanci irin wannan barna.(NAN)












































