Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu

Tunji Ojo new 750x430

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin bukukuwan Maulidi na shekarar 2025 domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa ranar Laraba a Abuja, ta hannun babban sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani.

Tunji-Ojo ya taya al’ummar musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murnar zagayowar wannan rana.

Ya bukace su da su yi tunani a kan kyawawan dabi’u na aminci, soyayya, tawali’u, hakuri da tausayi kamar yadda Manzon Allah Muhammad (SAW) ya nuna.

A cewarsa, wadannan dabi’u suna da matukar muhimmanci wajen gina kasa mai hadin kai, da wadata, da ci gaba.

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da addininsu ba da su yi amfani da wannan dama wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali.

Ya kuma bukaci ‘yan kasa da su marawa kokarin Gwamnatin tarayya baya wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ’yan kasa da su kasance masu bin doka da oda, da sanin tsaro, da kuma goyon bayan manufofin gwamnati da nufin tabbatar da jin dadin jama’a.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here