Gwamnatin tarayya ta fayyace rawar da take takawa a fannin kiwon Lafiya a matakin farko

Primary Healthcare Centre sabo 750x430

Gwamnatin tarayya ta jaddada irin rawar da take takawa a fannin kiwon lafiya a matakin farko na bayar da tallafi, inda ta nanata cewa alhakin kula da tsarin a fannin mulki ga cibiyoyin lafiya a matakin farko ya rataya ne a wuyan jihohi.

Dakta Muyi Aina, babban daraktan hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA), ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, a taron tattaunawa kan manufofin kudi na kiwon lafiya na kasa mai taken “Reimagining the Future of Health Financing in Nigeria”.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tattaunawar da hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) ta shirya na bukatar sake fasalin tsarin samar da kudade wanda zai sa harkar lafiya ta kasance mai dorewa, kuma mai isa ga dukkan ‘yan Najeriya.

Ya yi nuni da cewa, ana ci gaba da tattaunawa da Majalisar dokoki ta kasa domin kara yawan gudunmawar da gwamnatin tarayya ke bayarwa ga Asusun kula da kiwon Lafiyar Jama’a (BHCPF) fiye da kashi daya a halin yanzu da dokar Lafiya ta Kasa ta bayar.

Labari mai alaƙa: Za mu fara gudanar da aikin kula da marasa lafiya kyauta ƙarƙashin NEMSAS- AKTH

Da yake karin haske game da kokarin fadada abubuwan more rayuwa a cibiyoyin lafiya a matakin farko PHC, Aina ya bayyana cewa gwamnati na kara adadin wuraren da aka farfado daga 8,000 zuwa 17,600.

Shima da yake jawabi, Dr Oritseweyimi Ogbe, sakataren kwamitin sa ido na ministocin BHCPF, ya jaddada mahimmancin rikon amana da bayyana gaskiya wajen amfani da kudade.

A cewarsa, sabbin tsare-tsaren da aka bullo da su a karkashin BHCPF za su karfafa gudanar da harkokin kudi, da inganta amincewar al’umma, da tabbatar da cewa tallafin da ake bayarwa ya zama ingantacce na kiwon lafiya.

Ya kara da cewa ci gaba da hadin gwiwa da hukumar NHIA da abokan hulda zai taimaka wajen wayar da kan jama’a, aiwatar da aiki, da kuma shigar da al’umma cikin tsarin.

NAN ta ruwaito cewa masu ruwa da tsaki a taron sun jaddada bukatar ci gaba da bayar da shawarwari, jajircewa na siyasa, da kuma amfani da kayan aiki mai inganci don hanzarta ci gaba a fannin kiwon lafiyar Najeriya. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here