Gwamnatin jihar Kano ta fara shiri na musamman don yi wa akalla mutane miliyan 3.4 allurar rigakafin cutar COVID-19 a fadin jihar.
Tuni dai Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar ta bayyana cewa sama da mazauna Kano miliyan daya ne suka samu cikakkiyar alluran rigakafin tun lokacin da aka fara allurar a Kano.
Solacebase ta ruwaito cewa babban sakataren hukumar Dakta Tijjani Husseini ne ya bayyana hakan a yayin wani taron horaswa da aka shirya wa kwararrun kafafen yada labarai kan yakin wayar da kan jama’a kan rigakafin.
Dokta Tijjani wanda Daraktan Yaki da Cututtuka, Dr. Imam Wada Bello ya wakilta ya karyata zargin kin amincewa da allurar COVID-19 a Kano.
Yayin da yake jaddada cewa an samu gagarumin ci gaba a yawan mutanen da suka karbi allurar bisa radin kansu, Dakta Tijjani ya bayyana cewa, ana fama da matsalar rashin fahimtar juna a jihar.
Sakataren zartaswar ya ce, za a kai gangamin rigakafin zuwa kasuwanni, wuraren ibada, Masana’antu, Cibiyar Ilimi mai zurfi tare da goyon bayan kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yada labarai don rufe kashi 80 na al’ummar kasar.
Ya kuma jaddada cewa, za a baza ma’aikatan lafiya a sassa da kananan hukumomi baya ga wadanda ke jibge a manyan asibitocin jihar.