Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi kan yunƙurin kafa wata sabuwar majalisar dattawa a jihar da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa Consultative Forum (ACF) ke shirin yi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a yau Laraba.
Gwamnatin ta bayyana cewa tun a watan Janairun 2024 gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa Majalisar Dattawan jihar ta Kano, wato (KEAC) wadda za ta riƙa ba da shawara kan ci gaban al’umma.
Sanarwar ta ce, tun bayan sanar da kafa wannan majalisar, ana ci gaba da shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da ingantaccen tsarin da zai ba da damar fara aiki yadda ya kamata.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Wannan majalisar ba ta da wata alaƙa da siyasa ko jam’iyya, sai dai ta kasance dandalin bayar da shawara bisa hikima da gogewa.”
A cewar da, Majalisar za ta ƙunshi fitattun mutane daga Kano ciki har da tsofaffin shugabanni, alƙalan kotuna, malamai, sarakuna, ƴan kasuwa da shugabannin tsaro.
Gwamnatin ta kuma bukaci dukkan ƙungiyoyi da mutane su haɗa kai da tsarin da aka kafa maimakon kirkirar wani abu sabo.
A cewar ta, wannan zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan majalisar da tabbatar da cimma burinta na kawo ci gaba da haɗin kai ga jama’ar Kano.
Ta kara da cewa, nan ba da jimawa ba za a kammala tsarin kafa majalisar kafin gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da ita.
NAN













































