Hakimin Masarautar Zazzau ya rasu bayan ya halarci bukukuwan Sallah

Aminu Umar

Masarautar Zazzau ta yi rashin Hakimin Injiniya Aminu Umar.

Umar, basarake a Masarautar ya rasu ne bayan ya halarci dukkan bukukuwan Sallah.

Marigayi Injiniya Umar wanda kuma shi ne Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, shi ne zuriyar marigayi Sarki Dalhat daga masarautar Barebari ta Masarautar Zazzau.

A matsayinsa na Walin Zazzau, marigayi Injiniya Umar yana daya daga cikin manyan masu rike da mukamai a masarautar.

Shugaban Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai, mai kula da harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya bayar da tabbacin rasuwar a ranar Lahadi.

An ce marigayin ya halarci Hawan Daushe Sallah da aka yi a Zariya ranar Juma’a kuma yana daya daga cikin hakimai da suka kai wa Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli gaisuwar Sallah.

Marigayi Walin Zazzau ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya da dama.

Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Amaru da ke cikin birnin Zariya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here