Mutane uku sun rasu a jihar Nasarawa sakamakon zaftarewar kasa

d97bf381 5654 4854 96a7 3f0420ed134d

Mutane uku sun rasu yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon zaftarewar kasa da ya faru a yankin Keffi na jihar Nasarawa.

Shugaban Karamar Hukumar ta Keffi, Muhammad Baba Shehu shi ne ya tabbatar da hakan a wata hira da BBC.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu Kotun koli tabtabbatarwa da Abba gida-gida nasara

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Talata a lokacin da mutanen ke hakar yashi a wani wurin ɗibar yashi da ke unguwar Ayaba.

Nasarrawa na daga cikin jihohin kasar nan waɗanda ke da arziƙin albarkatun ƙasa.

Haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da a lokuta da dama kan haifar da mutuwar mutane saboda rashin ɗaukar matakan kariya da suka kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here