Majalisar Dattawa za ta gayyaci Wike kan karuwar satar mutane – Kingibe

majalisar, satar, mutane, rashin tsaro
Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya, Ireti Kingibe, ta ce majalisar dattawa za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan karuwar...

Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya, Ireta Kingibe, ta ce majalisar dattawa za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan karuwar rashin tsaro a Abuja.

A kwana-kwanannan ne dai aka samu karuwar masu garkuwa da mutane a Abuja.

Yayin da take bayani a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, ta bayyana cewa Majalisar Dattawa za ta gayyaci Wike da shugabannin hukumomin tsaro kan yawaitar laifuka a babban birnin kasar.

Karanta wannan: ‘Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a hanyar Abuja

Ta ce, “Lokacin da Majalisar Dattawa ta dawo, na shirya cewa kwamitin (Majalisar Dattawa) babban birnin tarayya na bukatar ya zauna da ministocin biyu da hukumomin tsaro domin su ba mu tsare-tsarensu na tsaro.

“Ba wai ina fata ba ne. Na san za a gayyace shi. Amma ko ya amsa ko bai amsa ba wani lamari ne na daban. Amma a matsayinsa na babban jami’in tsaro na FCT ya kamata ya yi shiri.

“Ya kamata ya iya gaya mana abubuwan da ya tanada wannan shi ne tsarin kare al’ummar babban birnin tarayya Abuja. Tsakanin sa, da kwamishinan ‘yan sanda, da shugaban DSS, dole ne su yi wani shiri.”

Karanta wannan: Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane a Abuja

Kingibe wacce ta yabawa hukumomin tsaro, ta kara da cewa akwai bukatar a yi aiki tukuru domin magance matsalar rashin tsaro a Abuja.

Ta kara da cewa, “Dole ne in yaba wa jami’an tsaro da suka yi wani abu a lokacin da muka fara korafi. Amma gaskiyar magana ta ɗan daɗe a baya, na yi ƙoƙarin jawo hankalinsu sai aka ce mini an wuce gona da iri, na ce ba zai yiwu ba saboda abin da nake gaya musu ban samu bayanai daga kafofin yada labarai ba, na samu ne daga mazaba ta.

“Suna ƙoƙarin ɗaukar shi duka da mahimmanci, amma akwai bukatar a yi da yawa. Kama masu garkuwa da mutane shine kawai alamar. Dole ne mu gano tushen abin da ke haifar da duk wannan rashin tsaro” A cewar Ireta Kingibe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here