Zamu daukaka kara – Abba Kabir Yusuf

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fito fili ya yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na soke nasarar da ya samu a zaben.

A cewarsa, an umurci kungiyar lauyoyin da ta daukaka kara kan hukuncin nan take.

SOLACEBASE ta ruwaito cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a ranar Laraba ta soke nasarar zaben gwamna Abba Kabir Yusuf kamar yadda INEC ta bayyana.

Kotun ta umurci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bayar Abba Kabir Yusuf tare da ba Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC sabuwar takardar shaidar cin zabe a matsayin zababben gwamnan jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here