Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana neman wasu ‘yan uwan juna biyu da ake nema ruwa a jallo bisa zarginsu da karbar N330m bisa zamba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta bayyana cewa, Faith Onoja mai shekaru 55 da Emmanuel Onoja mai shekaru 44, dukkansu daga karamar hukumar Ughelli ta Kudu da ke jihar Delta, EFCC na neman su.