Yanzu-Yanzu: Majalisar dokokin Kano ta gayyaci Murtala Garo don tantance shi a maysayin mataimkin gwamna

WhatsApp Image 2026 04 22 at 00.53.02 720x430

Majalisar dokokin Kano ta shirya tantance Murtala Sule Garo, a matsayin mataimakin gwamnan Kano a ranar Litinin 27 ga watan Afirilun da muke ciki.

Kakakin majalisar, Hon. Jibrin Ismail Falgore ne ya sanar da ranar da majalisar zata tantance Garon, bayan karanta wasikar da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aike wa majalisar a ranar Laraba, inda yake neman majalisar da ta tantance tare da amincewa da nadin na Garo.

Jaridar SolaceBase ta rawaito Gwamna Abba Kabir Yusuf yana son nada Murtala Sule Garo ne, biyo bayan saukar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo yayi a watan da ya gabata.

Ci gaban labari…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here