Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sabbin nade-nade a bangarorin ilimi ciki harda hukumar dake shirya jarrabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) da hukumar bunkasa ilimin fasaha ta kasa (NBTE).
Bayanin haka ya fito ta bakin babban mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, inda yace nadin wani bangare ne na kara karfafa bangarorin da ke karkashin ma’aikatar ilimi ta kasa.
Shugaban kasar ya nada Farfesa Modupe Adeola Adelabu a matsayin shugaban gudanarwar hukumar shirya jarrabawa kammala sakandire (NECO), ya kuma bar magatakarda Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi.
Haka zalika, shugaban ya ambaci sunan Farfesa Babatunde Salakoa matsayin shugaban hukumar gudanarwar hukumar bunkasa ilimin fasaha ta kasa (NBTE). Ya kuma sake nada babban sakararen ma’aikatar Farfesa Idris Bugaje a wa’adi na biyu na shekara biyar.
A bangaren kwalejojin kimiya da fasaha kuma, shugaban ya nada Bongfa Binfa a matsayin shugaban Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Tarayya N’yak-Shendam, da ke jihar Plateau a wa’adi daya shekara biyar. Binfa ya maye gurbin shugaban kwalejin na farko, Dr Mukaila Zakari Ya’u, wanda wa’adinsa ya kare a watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki.
Haka zalika, shugaban ya sabunta wa’adin Farfesa Chinwe Veronica Anunobi a matsayin daracta ganaral na laburaren kasa (NLN) na shekara biyar.












































